DANNA KASA DOMIN KALLON VIDEO
Shugaban jihar Katsina a Najeriya, Gwamna Dikko Umaru Radda, ya ce a shirye yake ya ba da ransa don magance matsalar ‘yan bindiga da ke haddasa fitina a jiharsa.
Gwamna Radda ya bayyana a wata hira da ya yi cewa bangaren tsaro na da matukar muhimmanci. Sun kafa doka don ƙirƙirar ƙungiyar sa kai waɗanda za su iya taimakawa jami'an 'yan sanda. Za a ba wa wadannan masu aikin sa kai makamai don kare kansu da sauran su.
